Goron Azumi: AZUMIN MASU CIKI DA MASU SHAYARWA: BY DR. IBRAHIM JALO JALINGO
AZUMIN MASU CIKI DA MASU SHAYARWA: Dr Ibrahim jalo jalingo 1. Farko dai: Maluman Musulunci sun yi Ittifaqi a kan cewa mace mai ciki da wacce take shayarwa idan suka ji tsoron cutuwar kansu, ko cutuwar kansu tare da cutuwar 'yan'yansu, to, suna da daman su bar yin azumin Ramadan, sannan daga baya su biya, babu kuma wata ciyarwa a kansu bayan biyan. 2. Abu na biyu: Su Malaman sun yi sabani game da: Idan ita Mai cikin, da Mai shayarwar suka ajiye azumi saboda tsoron kada 'yan'yansu su cutu, ba wai kada su su cutu ba. Sun yi sabani cikin wannan Mas'alah har zuwa kauli shida:- - Kaulin farko: Mai ciki da Mai shayarwa idan suka sha ruwa saboda tsoron kada 'ya'yansu su cutu, ba wai saboda su kansu su cutu ba, babu ciyarwa a kansu sai dai biya kawai. Wannan shi ne mazhabar Hanafiyyah. Da wasu Taabi'ai da Taabi'ut Taabi'in. - Kauli ba biyu: Ita mai ciki za ta biya ba tare da ciyarwa ba, amma mai shayarwa za ta biya, sannan kuma za ta ciyar. Wan...