Sudan: Al-Bashir ya sauka amma yana nan kan karagar mulki by ustaz yasir Ramadan gwale Kano

Sudan: Al-Bashir ya sauka amma  yana nan kan karagar mulki

Tun kusan lokacin da aka fara zanga zangar nuna adawa da tsadar kayayyakin masarufi a Khartoum Sudan, Albashir ya canja salon Gwamnatinsa, inda ya kori ministocinsa baki daya, ya kori mataimakin Shugaban kasa, ya yiwa Gwamnatinsa garambawul, domin fuskantar abinda zai faru yanzu.

Al-Bashir ya kwan da sanin abinda zai iya faruwa yanzu, kamar yadda ya faru. A hakika tun kusan shekarar 2015 ya nuna ya gaji da mulki a Sudan, amma sabida halin da yake ciki tsakaninsa da manyan kasashen duniya ya sanya dole ya kuma tsayawa zabe yaci.

A baya bayan nan da ake ta wannan zanga zanga, Al-Bashir ya fahimci cewar lallai karshen Gwamnatinsa ya zo, ko dai ya sauka kamar yadda yayi a yanzu, ko kuma a hambare shi ta karfin tuwo.

A lokacin da Al-Bashir ya tashi yiwa Gwamnatunsa garambawul, a gefe guda kuma yana kallon makomarsa da ta abokansa musamman wadan da ake nema ruwa a jallo a kotun duniya kan yakin da akai a Darfur a shekarar 2005, da kuma makomar Sudan a hannun wani wanda ba shi ba.

Shugaba Umar Al-Bashir da yake ya san mulki sosai, ya nada Ahmad Awad Ibn Auwf a matsayin mataimakinsa bayan da ya sallami Muhammad Hasabu Abdulrahman a matsayin mataimakin Shugaban kasa, sannan kuma ya nada sabon mataimakin nasa a matsayin ministan tsaro.

Shi wannan ministan tsaro kuma mai rike da mukamin mataimakin Shugaban kasa, wani abu ne mai nuna daman an san da wuyan biri aka daure shi a kwankwaso, sabida abinda ka iya zuwa ya dawo.

Domin kuwa, Albashir ya rikide daga Soja zuwa farar hula, amma ya dauko soja ya bashi mukamin mataimakinsa a cikin Gwamnatin demokaradiyya ta farar hula, kuma aka tabbatar da shi a matsayin ministan tsaro.

Waye Bin Auwf? Na farko dai shi Al-Bashir ya san kwanan zancen, yana yi yana kallon makomarsa. Dan haka sai ya dauko daya daga cikin jerin mutanan da ake nema ruwa a jallo a kotun duniya dake Hague.

Al-Bashir da tsohon mataimakinsa Ali Usman Muhammad Taha da yayi murabus tun a shekarar 2014, da kuma mutumin da ya karbi ragamar kasar a yanzu Ahmad Awad Bin Auwf dukkan su suna cikin jerin sunayen mutanan da ake nema ruwa a jallo game da yakin Darfur.

Dan haka tunda yake kotun duniya na nemansa wurjanjan, to, shi kansa Bin Auwf da ya karbi ragama har tsawon shekara biyu a yau, yana daga cikin mutanan da ake nema. A sabida haka babu wata matsin lamba da zata iya sanyawa a mika Al-Bashir zuwa kotun duniya bayan murabus dinsa.

Yanzu dai zamu iya fahimtar cewar Shugaba Umar Al-Bashir ya bar mulki amma kuma a badini yana cikin Gwamnatin tsundum, domin bayan shekara biyu dole ne Al-Bashir da shi Bin Auwf zasu dasa yaransu da zasu karbi iko ba tare da sun mika su ga kotun duniya ba.

Dan haka, har yanzu tsugune bata kare ba a Sudan. Masu zanga zanga bayan sun dawo hayyacinsu, zasu sake dawowa kan tituna domin nuna adawa da shi wannan Ahman Awad Bin Auwf din. Sai dai kuma idan Gwamnatin ta aiwatar da sauye sauyen da zasu saukaka al'amura wanda abu ne mai wuya.

Yasir Ramadan Gwale
11-04-2019

Comments

Popular posts from this blog

MEKE FARUWA A KANO: By Dr. BELLO GALADANCHI KANO

Shin Ya dace Bulama Bukarti Ya kira abinda Bauchi state Governor ya fada da wawanci? By: Muhammad Shu'aibu Gunda

WAIWAYE ADON TAFIYA (4) by USTAZ ABDURRAHAMAN MUH'D SANI RIJIYAR LEMO