Kungiyar IZALA zata sakawa mutum 120 hannuwa da kafafun roba kyauta a jahar Kano
Kungiyar IZALA zata sakawa mutum 120 hannuwa da kafafun roba kyauta a jihar Kano
Daga Ibrahim Baba Suleiman
Kungiyar IZALA naci gaba da aikin samawa mutane kafafu da hannuwan roba kyauta wanda akayiwa suna da (MSIC). Shirin Wanda ke tafiya a halin yanzu a jihar kano karkashin jagorancin shugaban IZALA Sheikh (Dr) Abdullahi Bala Lau da hadin gwuiwa da Tolaram Foundation na kasar India, tare da hadin gwuiwar Gwamnatin jihar kano.
Sheikh Lau ya kai ziyarar gani da ido a wajen aikin dake gudana a Asibitin kwararru na Muhammadu Buhari Specialist dake Giginyu Kano
Sheikh Bala Lau ya sami mara bayan shugaban kungiyar na jihar Kano Dr. Abdullahi Sale Pakistan, A wannan karon mutane 120 suka sami moriyar wannan aiki. Kwamishinan aikin lafia na jihar Kano shima ya sami ziyartar wajen da aikin ke gudana a madadin mai girma Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan