JINANNAN AL'UMMAR MUSULMIN AREWACIN NIGERIA.... BY USTAZ HAMISU NASIDI BABAN AUWAAB
JINANNAN AL'UMMAR MUSULMIN AREWACIN NIGERIA...
Tun kusan shekarar 2011 lamarin zubar da jinin musulmin Arewacin Nigeria yayi fara kamari, inda lamarin ya ta'azzara a shekarar 2013 zuwa 2015.
Yan siyasa sunyi Campaign sosai da Lamarin Tsaro da ya Addabi Al'ummarmu, wannan yasa Muka tsani Gwamnatin da ta shudi mukai Rubdugu wajen zaben gwamnati mai ci a yanzu, har Allah ya bata Nasara.
Godiya ta tabbata ga Allah gwamnati tayi Kokari sosai wajen Dakile Barnar zubar da jinin Al'umma, da tashin Bama bamai a ko ina a cikin arewacin kasar nan.
Babbar Fitnar da take Addabarmu a yanzu dai itace ta zubar da jini, musanman a Jahohin Zamfara, Sokoto, Kebbi, da kuma katsina. Ga kuma fitnar sace mutane da neman kudin Fansa, wadda ake yi wadancen jahohi da na Ambatax da kuma karin wasu jahohin kamar su kaduna, Taraba Beneau da Sauransu.
A wancen lokacin Al'umma sun dage da Addu'o'i ba dare ba rana, Malamai sun ta Nasiha da jan hankalin Gwamnati, wasu Malaman sun ta zubda hawaye suna kuka sabida tsabagen tausayin rayukan da ake kashewa.
A wannan Lokacin ma muna kira ga Gwamnati dan Allah a kara kaimi akan wannan lamari na tsare jinin Al'umma da Dukiyoyinsu, Muna kara kira ga Malamai musanman wadanda suka bada Gudunmuwa a wancen Lokacin, Yanzu ma Lokaci ne da ya kamata ku cigaba da yiwa Gwamnati Nasiha akan wannan Lamari, ku cigaba da yi mata kuka a mimbarorinku da wuraren wa'azozinku, dan munga tasirin Abinda kukayi a Gwamnatin baya.
Wadanda ake kashewa a yanzu suma Yan Uwanku ne Musulmai suna da Hakkin akanku na kuyi masu abinda kukayi a baya har a samu mafita.
Allah ka zaunar mu Lafiya.

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan