WAIWAYE ADON TAFIYA (4) by USTAZ ABDURRAHAMAN MUH'D SANI RIJIYAR LEMO
Akwai fa'idah daure ka karanta harkarshe.
WAIWAYE ADON TAFIYA (4)
____________________________
____________________________
A watan da ya gabata ne Musulmai kimanin mutun 51 suka rasa rayukansu, sama da mutum 20 kuma suka ji rauni bisa wani mummunar hari da wani dan ta'adda ya kaiwa Musulman a kasar New Zealand, an yi ta rubuce rubuce akan batun sai dai banga wanda yayi cikakken bayani game da wasu alamu da suka bayyana na wasu sunaye da shekaru da wanda ya aiwatar da ta'addancin ya rubuta a jikin Makaminsa ba, da kuma videon da ya dauka da kansa, hakan tasa naga yakamata in yi tsokaci akansu wasu daga ciki da kuma sakwannin da suke isarwa.
1- Wakar Serbia Strong: ko Remove the Kebab itace wakar da ya kunna a farkon videon da ya dauka da hannunsa a hanyarsa ta zuwa aiwatar da ta'addancinsa. Waka ce da wasu sojojin Serbia sukayi ta don karfafa gwiwar 'yan uwansu sojoji a yakinsu da Bosnia da kuma neman yardar Radovan Karadžić wanda ya jagoranci yiwa Musulmai kimanin dubu Takwas(8,000) kisan kiyashi a garin Serbrnica a Bosnia a shekarar 1995. a watan da ya gabatane kotun manyan laifuka ta duniya(ICC) ta yankemai hukuncin daurin rai da rai.
2- Anton Lundin Pettersson: matashine mai kimanin shekara 21 dan kasar Sweden. Ranar 22/10/2016 ya shiga wata makaranta ta Musulmai dauke da takobi a hannunsa ya hau dalibai da malamai da sara hakan yayi sanadiyar rasa rayukan dalibai 3 da malami 1 da raunata wasu da dama, nan danan 'yan sanda suka zo suka nemi ya mika wuya yaki shine suka harbeshi karshe ya cika a gadon asibiti.
3- Alexandre Bissonnette: matashine dan kasar Canada a ranar 29/1/2017 ya afkawa wani masallaci da harbi bayan an gama sallar Isha'i wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan masallata 6 da raunata mutum 17. Karshe dai bayan an kamashi aka yankemai hukuncin daurin rai da rai sabo da kasar Canada bata amfani hukuncin kisa, lokacin wasu sunyi kokarin nuna cewa ai ba muslmai ya nufa ba kawai dai yana adawane da baki. Sai dai in muka duba zamu ga cewa shima ba dan asalin Canada bane bakone dan France, kuma a Canada akwai ungwannin baki da yawa kamar yan Spain yan Mexico da sauransu amma sai bai nufesu ba sai ya nufin musulmai kawai.
4- Skanderbeg: Wani basarakene dan Kasar Albania da ya yi ridda yakoma sunansa na asali George Castriot ,ya yiwa daular Usmaniyya tawaye bayan ya nemi taimakon papa Roma wato pope Pius II (na biyu) a shekarar 1444 CE, ya shiga yaki 13 da sojojin Daular Usmaniyya lokacin mulkin Sultan Muhammad II (Na biyu) wanda ake mai lakabi da Alfatih duk yayi nasara a kansu, sai da akayi ta dauki ba dadi tsawon shekara 25 an kasa cin masa sai bayan rasuwarsa a shekarar 1468 CE sannan ne muslmai suka iya dawo da kasar Albania karkashen su.
5- Marco Antonio Bragadin:Sarkin garin Famagusta a tsibirin Cyprus lokacin da daular Usmaniyya ta mamaye tsbirin a kokarinta na bawa Qustatiniyya (Istanbul a yannzu) ta yiwa garin Famagusta kawanya an yi ta dauki ba dadi tsakanin su da shi harma ya kama wasu sojojinsu a matsayin firsinonin yaki shine aka shiga tattaunawa tsakaninsa da Muslmai don ganin ya saki wadanda ya kama, da abun yaki ci yaki cinyewa muslmai sukayi nasarar shiga garin a shekarar 1571 CE sai dai sun tarar ashe daman can tun a ranar da wannan sarki ya kama wadannan firsinoni ya kashesu daman kawai wasa yake musu da hankali don ya bata lokaci ko wala'alla zai samu agaji. Karahe dai kwamandan tawagar Muslmai Mustafa Basha ya kasheshi bayan ya yanke kunnesa da hanncinsa da fedesa a mataki na daukan fansa ga sojojinsa.
6- 1683 Vienna : lokacin ne Daular Usmaniyya ta nufi bude garin Austria har ta kai ga babban birnin wato garin Vienna wanda sukamai kawanya amma basu samu nasar cin garin ba,sun kuma yi asarar sojoji sama da 15,000. Wannan shine yunkuri na karshe da Daular Usmaniyya tayi wajen kara fadada a nahiyar Turai tun daga wannan lokacin har rushewarta a 1922 CE bata kara wani yunkurin kutsawa nahiyar Turai ba.
7- Tours 732: yakine da ya auku zamanin daula Umawiyya a shekarar 732 CE (114 Ah) tsakanin Muslmai karkashin jagorancin Tabi'i Abdurrahman Alghafiqy da Sarkin Faransa Charles Martel a kasar Faransa ,Sai dai muslmai basu samu Nasara ba harma Abdurrahman din yayi shahada, yakine shine yunkurin karshe da muslmai su kayi na kutsawa nahiyar Turai ta yamma.
8-Charles Martel: Sarkin France da ya ci nasarar dakatar da Musulmai a yakin Tours ko Baladush shuhada a wurin Musalmai.
9- Acre 1189: lokacin ne Sarkin England Richard the Lionheart shi da tawagarsa ta Third Crusade suka kashe muslmai kimanin 2000 a garin Acre a Palestine.
10- 1571 :a shekarar akayi yakin Lepanto tsakanin Daular Usmaniyya da hadakar kasashen Kirstoci na Turai kuma karshe daular
Usamniyya bata ci nasara ba.
11- 1688 :kubucewar babban birnin Serbia Belgrade daga hannun Muslmai bayan zazzafan yaki.
Akwai sunaye da yawa bayan wadannan kamar su David soslan, Divid of Georgia IV, Dmitry Sinaffin, Serban Cantacuzino, Admiral Edward Codrington, Sebastiano Venier da sauran sunaye wanda duk suna da alaka da tarihi da addinin kirstanci . A iya wadannan sunayen zamu fahimci cewa ba da radin kansa ya aikata abinda ya aikata ba ,akidace yake da ita a zuciyarsa ta kiyayya da adawa da Musulmai ta hanyar halarto yake yaken da suka faru da koyi da wadancan mutane da ya rubuce makaminsa da sunayensu.
abin la'akari anan shine yadda yake matashi dan shekara 28 amma yake dauke da wadannan tarihe tarihan,wannan misalin dayane daga cikin al'ummar da har gobe take rike da tarihinta sannan a duk sanda suke shirin yakar Muslmai sai sun halartoshi, a gefe guda kuma babu al'ummar da ta watsar da nata tarihin ta banzatar da shi kamar Muslmai in da zaka tambayi wani matashi musulmai game da rabin wadannan bai sani ba, amma yasan sunayen mawaka, ya kwallo, yan film da sauran mashrimata bila adadin, Wanda anan kawai zamu fahimci irin dimuwar da al'ummar Musulmai take ciki.
Tarihi shine madubin rayuwar ko wace al'umma. duk al'ummar da bata san da dinta ba to bazata taba tsinana wani abu a yau dinta ba balle ta san ya gobenta zata kasance. Sanin hakane ma yasa makiyanmu suke rike nasu tarihin hannu biyu suke bawa 'ya'yansu suke kuma kokarin mantar damu da yanke alakarmu da namu tarhin da kirkirar mana wasu shashashu a matsayin sune gwarazan mu abun koyi gare mu wannan itace babbar illa da suka mana.
#Tarihinmu_madubinmuAlgundawy.wordpress.com

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan