MEKE FARUWA A KANO: By Dr. BELLO GALADANCHI KANO

Assalamu alaikum. Yau ina so nayi kira ga jama’a a goya mun baya a sabuwar gwagwarmaya domin neman amsa da jawo hankula dangane da yawan rashe-rashe da ake fama da shi a Kano a halin yanzu. A cikin awa 24 kacal, na rasa yan uwa sun fi hudu, sannan a shafin facebook na ga sanarwa sun fi ashirin na rasuwa daga jama’a daban daban, kuma duk a Kano.

A makon baya, mun rasa matar ma’aikacin gidan mu, kuma an kira NCDC wato Hukumar Yaki da Cututtuka masu Bazuwa, da ta zo ta duba, amma tayi kunnen uwar shegu har washe gari. Gwamnatin Kano tace karya ne, babu mace mace kuma ta saka hannu akan dokar hukunta duk wanda ya yada jita-jita. Wadanda suka rasu kawai binne su ake yi ba tare da an san mene ne takamai-mai ya same suba.

Muna so mu jawo hankalin duniya akan wannan lamari. Ya kamata a yi wani abu akai. Kar muyi shiru, mu zo muna da na sani. Abun ya fara yawa, kuma wa ya san inda zai tsaya?

-Mene ne amfanin ilimin mu idan baza mu iya banbance gaskiya da karya ba?
-Mene ne amfanin hankalin mu idan baza mu iya yin abunda ya kamata ba domin kare ‘yan uwan mu da abokan arziki ba?
-Mene ne amfanin wayoyin mu idan baza mu iya amfani da su don yin gyara ba?
-Mene ne amfanin muryoyin mu idan baza mu iya amfani da su muyi magana ba?
-Mene ne amfanin ‘yancin mu idan baza mu iya amfani da shi mu kau da zalunci ba?
-Mene ne amfanin tsoro idan har muna ji muna gani mutanen mu dayawa suna mutuwa kullum, in banda addu’a babu abunda zamu iya yi?

Ai ko Manzon Allah SAW sai da ya dauki takobi ya fita yayi yaki da rashin imani da zalunci. Idan muka shiru, mun zama matsorata, kuma mun goyi bayan rashin-ko-in-kula da akewa jama’a a Kano.

Takobin mu shine wayar dake hannun mu, kuma yawan mu shine tagomashin mu. Baza mu iya fita ba, amma za’a iya jin muryoyin mu a duk fadin duniya.

Ina kira ga duk wanda zai iya musamman maza (mata zaku iya rufe fuska), a dauki takarda a rubuta akai “ME KE FARUWA A KANO?”, a dauki hoto da shi, a buga akan duk shafukan da zai iya bugawa. Tunda an hana fita, ai daga cikin gida ma zamu iya daukar mataki mu jawo hankali domin kiyaye rayuka da lafiyar ‘yan uwa da abokan arziki.

Dr. Bello Galadanchi

Comments

Popular posts from this blog

Shin Ya dace Bulama Bukarti Ya kira abinda Bauchi state Governor ya fada da wawanci? By: Muhammad Shu'aibu Gunda

WAIWAYE ADON TAFIYA (4) by USTAZ ABDURRAHAMAN MUH'D SANI RIJIYAR LEMO