Posts

Showing posts from March, 2019

Khudubar masjidis salafiyya Biu by Sheikh Abubakar bin Mustafa (Topic) Abinda ya faru A Shekara ta 597 &524 Hijiriya...?

Image
KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: 🌐22/RAJAB/1440HJRY 🌐29/MARCH/2019MLDY 🎙MAI GABATARWA👉 Abubakar BN Mustafa Biu ♦TOPIC👉🏻  [ABINDA YAFARU A SHEKARA TA 597 & 524 HJRY] ◼NA KASASHI GIDA👉 8⃣ 1⃣👉MUQADDIMA‼    Yaku bayin ALLAH! lalle bala'i baya sauka saida zunubi Kuma ba'a daukewa saida tuba, duk masifunda ke samunmu ayau don zunubbanmu ne, ALLAH yana saukarwane don mutuba, wanda bai tuba ba kuma sai WUTA a lahira, 2⃣👉 HADITSAR SHEKARATA 597-HJRY‼  ⬛IBN KATSEER yace= a wannan shekarata 597 kaya yayi matukar tsada a kasar MISRA, mawadata da talakawa dayawa suka mutu sakamakon yunwa,    ABU SHAMAH cikin littafin (AZZAIL) yake cewa= a wannan shekara AL-ADIL yayiwa gawarwaki 220,000 likkafani a dukiyarsa dasuka mutu a wata daya, don yunwa anci karnuka da mushe a MISRA, anci naman mutane manya da yara, har yakaiga iyaye suna soya naman 'ya'yansu suci a bayyane ba mai muzanta haka don yazama ruwan dare, da kananan yara suka kare...

WA YA SAN GOBE BANDA ALLAH BY SHEIKH ALIYU SA'ID GAMAWA

Image
WA YA SAN GOBE.??? Nasihar wanna Rana ta Jumma'ah Allah cikin hikimar sa ya boye mana sanin gaibi, da  damar sanin mi zai faru gobe, hakanan ba wata rai da ta san ranar ajalin sa ko garin ajalin sa. Kuma mu  tuna fa cewa: Samu da rashi, wato yalwa da rashi ko juyawar yau da gobe duk naga Allah shi kadai ubanginjin talikai. Mu  'yan adam buri garemu da yawan tanadi, ga kwadayi da son mu samu mu tara, gamu da sha'awa a ciki da wajen zukatan mu, da sauran bukatun dan adam a rayuwa. Hakika rashin sanin abinda zai faru gobe rahama ne ga dan adam kuma darassi ne garemu cewa muyi taka tsan-tsan da wannan rayuwa, mu yiwa kan mu tanadin alheri duniya da lahira. Ya kai dan uwa na, kada ka wulakata wani baka san gobe mi zai zama ba. Kada ka tozarta addini don baka san kana wani aiki mutuwa zata riske ka ba. Kada kaci haramun don baka san miye abincin ka na karshe ba. Kowa ya nisanci alfasha da miyagun aiyuka don bawanda yasa aikin sa na karahe. Muyi don Allah mu ...

Allah ya kubutar da malam koda munafukai basa so.!!

Image
Alhamdulillah!!! Allah shine Abun godiya... Munafukai sunji kunya ta Allah ba tasu ba. Allah mungode maka da wannnan ni'ima a garemu da kayi, na tseratar da Alaramma Ahmad sulaiman, da tawagar sa. Muna godiya kwarai ya Allah a bisa wannan, mun shiga cikin tashin hankali mu da shuwagabanin da mutani da dama Wanda musulinci ne gaban su ba munafurci da yaudara ba. Munga Abu kala-kala ta sanadin faruwar haka, wasu sunyi farin ciki da hakan!.. A yayin da wasu jama'ah masu yawa sukayi ta bakin Ciki da tashin hankali kan faruwar haka!! Sukan sanya malam cikin Addu'o'in su na alkhairi da sauran tawagar malam, dama sauran yan'uwa musulmai, da Akayi garkuwa dasu. Irin wadan nan mutani ba Abunda zamuce dasu sai Allah ya saka musu da alkhairi ya biyasu da mafificin saka mako, wato al'jannah. Allah ya kiyaye faruwar haka nan gaba,  ya Kare mana sauran malamai da Alarammomin mu baki daya Amin.

Khudubar masjidis salafiyya Biu by Sheikh Abubakar bn Mustafa Biu

KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: 🌐08/RAJAB/1440HJRY 🌐15/MAY/2019MLDY 🎙MAI GABATARWA👉🏻 Abubakar BN Mustafa Biu 🔸TOPIC👉🏻 [😭KUKAN ZUKATA❣DAGA WUTA HURARRIYA♨] ➖NA KASASHI GIDA 🔟 1⃣➖MUQADDIMA➡    Lalle WUTA halittace mai kuna daga halittun ALLAH, bata karewa tazama babu, ALLAH ya tanadarda ita ga masu sabawa umurninsa da na Manzanninsa, Wanda yaji tsoronta a duniya yanemi tsari daga gareta da nisantar sabon ALLAH za'a amintar dashi daga gareta, Wanda baiji tsorontaba yasabawa ALLAH za'a firgitashi ita a kiyama Kuma akonashi acikinta😭 2⃣➖DAGA SIFFAR WUTAR➡  💡ALLAH SW yace <<WUTACE hurarriya>>  💡ALLAH SW yace <<WUTACE mai kuna>>  💡ALLAH SW yace <<WUTACE mai babbakewa>>  💡ALLAH SW yace <<WUTACE makamashinta mutanene da duwatsu>> 3⃣➖SIFFAR 'YAN WUTA ACIKIN WUTAR➡  💡ALLAH SW yace <<Ranarda za'a jasu acikin WUTA bisa fuskokinsu- kudandani sh...

Matsalar garkuwa da mutane ba Abun bayyanawa A kafafen yada labarai bane

Image
Matsalar  Garkuwa Da Mutane Ba Abun Bayyanawa A Kafafen Yada Labaru Bane Daga Mahmud Isa Yola Yayinda kungiyar IZALA ta kasa ta dukufa da kokarin an ceto shahararren mahaddacin Al-Kur'ani mai girma,  Sheikh Ahmad Suleiman daga hannun 'yan ta'adda,  wasu sun dauki alkalami suna rubutu marasa dadi akan kungiyar da shugabannin ta,  ta hanyan chakuda bayanai wadanda fitar da su fili kuskure ne babba. Zan bada misali: lokacin da akayi garkuwa da 'yan agaji na Izala bangaren Jos,  Edita na ya umurce ni da in hada labari akai. Nayi kokarin samun Sheikh Sani Yahya Jingir a waya ban same shi ba,  cikin ikon Allah tsohon abokin aiki na ya hada ni da Shehin Malami Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun nayi hira da shi. Mun tattauna abubuwa da dama akan wadannan 'yan agaji,  na fahimci abubuwa da dama,  daga karshe kafin in ajiye waya sai da mukayi ittifaki cewa yayata abun da ya shafi Kidnapping da kuma sanya maganan manyan shugabannin siyasa ko malamai a ci...

Rayuwar ka A social network riba kake samu ko Akasin haka.!!!

Image
Internet, ko social media. Dukanin su zamu iya daukan akan Abu guda.! Domin sai da “internet" za'ayi social network, ko kuwa mukun iya cewa Internet ita ta haifi dukkanin wasu social network, saboda ganin muhimmancin wadan nan kafa. Wanda yanzu zamu iya cewa kusan, kowa yana ta'amuli da wadan nan Abubuwa, kodai ya kasance yana da. Shafi A Facebook ko kuma A WhatsApp ko kuma Instagram, DSS. Toh ganin hakan ne ya sa nayi wannan nazari, domin tunatar da juna... Shin idan za'a tambaye ka me kake anfana dashi sanadin, ta'amali da kafar sadarwa? Wani irin amsa zaka bada, cewa zakayi “zero ba komai nake samu ba" kada ka kuskura ka bada wannan amsar. Domin kayi hasara, ko ba komai kamata yayi ka Dan lissafa cewa INA karuwa ta hanyoyi masu yawa idan Akace kadan daga cikin su  1. Ina karuwa ta fannin Addini NA  2. Rayuwata karatun zamani da kuma sanin yanda duniya take ciki. Toh ko ba komai Dan'uwa kayi ribar zuwan ka. Nan domin zai taimake ka lahiran ka da dumi...

Rayuwa ta.!!

An haifeni A Shekaran (1996 12-3) A wani kauye, da Ake kira da Kalong A Shendam local gamnan Area, A jahar pilato in'da na fara karatu A nursery school, nawa A makaranatar Sheikh Abubakar gumi Wato [G.S.S. Yelwan shendam] Daga bisani na dawo Biu L.G.A A borno state. Bayan fadace-fadacen da suka faru A 2000 zuwa 2003. Sai hakan yayi sanadiyar dawowa ta jahar borno, in'da nazo na cigaba da karatu na Anan kuma ina tare da mahaifana guda biyu. Nayi karatu Amma ban kammala secondry na ba. Sai cikin wannan shekaran da muke cikin ta wato #2019 insha Allah. Nake sa ran gamawa da kuma burin, cigaba da karatu. Wanda yanzu haka ina kasuwan ci. Wannan shine kadan daga cikin tarihin rayuwata kenan.