Khudubar masjidis salafiyya Biu by Sheikh Abubakar bn Mustafa Biu
KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐08/RAJAB/1440HJRY
🌐15/MAY/2019MLDY
🎙MAI GABATARWA👉🏻 Abubakar BN Mustafa Biu
🔸TOPIC👉🏻 [😭KUKAN ZUKATA❣DAGA WUTA HURARRIYA♨]
➖NA KASASHI GIDA 🔟
1⃣➖MUQADDIMA➡
Lalle WUTA halittace mai kuna daga halittun ALLAH, bata karewa tazama babu, ALLAH ya tanadarda ita ga masu sabawa umurninsa da na Manzanninsa, Wanda yaji tsoronta a duniya yanemi tsari daga gareta da nisantar sabon ALLAH za'a amintar dashi daga gareta, Wanda baiji tsorontaba yasabawa ALLAH za'a firgitashi ita a kiyama Kuma akonashi acikinta😭
2⃣➖DAGA SIFFAR WUTAR➡
💡ALLAH SW yace <<WUTACE hurarriya>>
💡ALLAH SW yace <<WUTACE mai kuna>>
💡ALLAH SW yace <<WUTACE mai babbakewa>>
💡ALLAH SW yace <<WUTACE makamashinta mutanene da duwatsu>>
3⃣➖SIFFAR 'YAN WUTA ACIKIN WUTAR➡
💡ALLAH SW yace <<Ranarda za'a jasu acikin WUTA bisa fuskokinsu- kudandani shafar saqar>> (SRT QAMAR= 48)
💡ALLAH SW yace <<zamu tashesh akiyama akan fuskokinsu bebaye kurame makafi>> (ST ISRA'I= 97)
💡ALLAH SW yace <<idan WUTAR tahangosu daga nesa sai suji tana gurnani>> (SRT FURQAN= 12)
4⃣➖ABINCIN 'YAN WUTA➡
Abincinsu kala 4 ne=
¹💡ALLAH SW yace <<lalle itacen ZAQUM* Abincin masu zunubine* kamar narkakken kwalta* tana tafarfasa aciki* kamar tafarfasar ruwa mai matukar zafi>> (SRT DHN= 43-46)
²💡ALLAH SW yace <<basuda abinci sai DARI'IN>> (SRT GASHIYA)
³💡ALLAH SW yace <<mun tanadi mari da WUTAR Jaheem* da abinci mai makurewa>> (SRT MZML= 12-13)◼IBN JUBAIR yace= duwatsune na ashana◼IBN ABBAS yace= Lomace ta kaya, koda gayane ta tokare wuya bata wuceba kuma bata komaba tana iya barazanar kisa- to me kuke zato in yazanto kaya ne‼
⁴💡ALLAH SW yace <<basuda abinci sai GISLEEN>> shine lakan diwa da mugunyar 'yan WUTA,
5⃣➖ABIN SHAN 'YAN WUTA➡
💡ALLAH SW yace <<in sun nemi agaji za'a agaza musu da ruwa kamar narkakken kwalta zai soye fuskokinsu, tir da wannan abin shan>> (SRT KHF= 29)
💡ALLAH SW yace <<za'a shayar dashi daga ruwa diwa, zai rika kwankwada bazai iya hadiyewa kuma mutuwa yazo masa ta ko'ina amma bazai mutuba kuma bayansa akwai azaba mai kauri>> (SRT IBR= 15-17)
6⃣➖TUFAR 'YAN WATA➡
💡ALLAH SW yace <<tufarsu na narkakken harsashine>> (SRT IBR= 50)
💡ALLAH SW yace <<acikin Jahannama sunada shimfidin WUTA asamansu kuma mayafin WUTA>> (SRT A'ARAF= 41)
7⃣➖KUKAN 'YAN WUTA➡
💡ANNABI SAW yace "lalle 'Yan WUTA zasuyi kukan hawaye sa'annan suyi na jini"
8⃣➖NARKON ZAFIN WUTAR➡
💡ANNABI SAW yace "wutan duniya 1 bisa 70 ne na WUTAR lahira kuma aka kasa dayan gida 100, daya bisa darin daya bisa sittin din shine na duniya"
9⃣➖'YAN WUTA DA ROKON ALFARMAR MALIKU➡
💡ALLAH SW yace ga 'yan WUTA <<zasuyi kira suce YA MALIKU- ubangijinka yakashemu mana, sai yace kufa zama zakuyi acikinta>> (SRT ZHRF= 77) ◼Malaman Tafsiri sukace= in sun roki alfarmar awurinsa sai anyi daruruwan shekaru kafin yabasuma wannan amsar‼
🔟➖DAGA LABARIN MASU KUKAN TSORON WUTA TUN ANAN DUNIYA➡
◼HASANUL BASARY yace= Don tunawa da WUTA Salihai sunyita kuka harma wasunsuma sun mutu don tunata‼
◼ALIY IBN FUDWAIL IBN IYAD yana kiyamullaili yana karanta fadin ALLAH SW💡👉🏻
<<inama da zakaga lokacinda aka tsaidasu akan WUTA- suna cewa kaitonmu inama da za'a mayar damu duniya bazamu sake karyata ayoyin ubangijinmuba>> (SRT AN'AM= 27)
yanata maimaita ayannan har ransa yafita‼Mahaifinsa FUDWAIL yazo yana cewa= ya Dana wanda WUTA yakasheshi❗Wallahi ba abinda yarona sai tsoron azabar ALLAH‼
◼YAZEED AL-RAQASHY- ana masa don yawan kukansa akace masa= koda don kai kadaine aka halicci WUTA ai kukannaka bazai iya wuce hakaba⁉Sai yace= ai an halicci WUTANE don ni da 'yan uwane mutane da aljanu, shin bakuji fadin💡ALLAH SW dayake cewa <<zamu bada lokaci don hisabinku yaku mutane da aljanu>>
◼MALIK IBN DINAR tace= da za'a shugabantar dani akan Mutane da na ware wasu Mutane aikinsune shine aikinsu shine suhau hasumiyoyin gari suyi tayiwa mutane shela suna cewa= WUTA‼WUTA‼
◼Har Yanzu MALIK IBN DEENAR= yaga wata baiwa tun bayan isha'i har zuwa asuba tana dawafi a ka'aba🕋 ba abinda take cewa da nanatawa sai <YA UBANGIJINA! MEYASA BAKADA ABINDA ZAKA AZABTARDA WANDA YASABA MAKA SAI DA WUTAAA‼
👏YA RABBANA! DON TAUSAYINKA KATSAREMU DAGA SHIGA WUTA😭
👏YA RABBANA! KAKUBUTARDA SU ALARAMMA AHMAD SULAIMAN DAGA HANNUN MASU GARKUWA CIKIN LAFIYA DA AMINCI😭
AMIIIIIIIIIIIIIIIIN👏👏👏
via👉🏻 Abubakar BN Mustafa Biu✍
Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan