Matsalar garkuwa da mutane ba Abun bayyanawa A kafafen yada labarai bane
Matsalar Garkuwa Da Mutane Ba Abun Bayyanawa A Kafafen Yada Labaru Bane
Daga Mahmud Isa Yola
Yayinda kungiyar IZALA ta kasa ta dukufa da kokarin an ceto shahararren mahaddacin Al-Kur'ani mai girma, Sheikh Ahmad Suleiman daga hannun 'yan ta'adda, wasu sun dauki alkalami suna rubutu marasa dadi akan kungiyar da shugabannin ta, ta hanyan chakuda bayanai wadanda fitar da su fili kuskure ne babba.
Zan bada misali: lokacin da akayi garkuwa da 'yan agaji na Izala bangaren Jos, Edita na ya umurce ni da in hada labari akai. Nayi kokarin samun Sheikh Sani Yahya Jingir a waya ban same shi ba, cikin ikon Allah tsohon abokin aiki na ya hada ni da Shehin Malami Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun nayi hira da shi.
Mun tattauna abubuwa da dama akan wadannan 'yan agaji, na fahimci abubuwa da dama, daga karshe kafin in ajiye waya sai da mukayi ittifaki cewa yayata abun da ya shafi Kidnapping da kuma sanya maganan manyan shugabannin siyasa ko malamai a ciki matsala ne babba zai janyo ga wadanda akayi garkuwa da su.
Rahoton yana nan an wallafa a jaridar Rariya, Daily Nigerian Hausa da kuma Leadership Hausa. Masu bukata suna iya nema su karanta.
Ko a cikin rahoton, bayanai da na rubuta basu da yawa, duk da cewa mun tattauna akan abubuwa da dama, ba komai ya sa hakan ba sai saboda matsalar tsaro na wadanda suke hannun miyagun a wannan lokaci.
Yayinda da dama daga cikin mu muka dukufa da addu'a muna dakon lokacin da zamu ji an saki Alaramma Ahmad Suleiman, wasu sun dage da jifan kungiya da miyagun maganganu saboda dalilan da su suka fi sani.
Munaso duniya ta sani cewa, kungiyar Izala tana iya kokarin ta, kuma babu wanda zai tilasta kungiya ta fadi abun da take yi saboda babu dacewar hakan ko kadan. Kazalika jama'a su sani cewa, shugabannin mu sun fi mu rudewa da tashin hankali akan wannan matsalar, amma su malamai ne ba zuwa zasuyi suna kawo kukan su Facebook da WhatsApp ba, sai dai su kaiwa Allah Madaukakin Sarki.
Bayan kasancewa na dan jarida, dadama a nan sun san ni dan Izala ne kuma nasan zaku yadda da ni idan nace muku kungiyar Izala tana iya kokarin ta. Haka kuma ni dalibin shugaban kungiya na kasa Sheikh Dr. Imam Abdulullahi Bala Lau ne, dukkan karatukan sa ni nake dauka, nasan zaku fahimce ni idan nace muku Sheikh Bala Lau duk yafi mu damuwa da a saki Alaramma ta duk wani hanya da zata yuwu.
Sheikh Bala Lau mutum ne mai matukar tausayi da dattaku, mu hadiman sa babu wanda baya mutuntawa iya mutuntawa. Babu yanda za'ayi Sheikh Bala Lau ko wani daga cikin malamai ya samu kwanciyar hankali alhalin babban alaramma na kungiyar yana hannun 'yan ta'adda fitinannu.
Muna kira ga jama'a suyi watsi da maganganun wadannan mutane, muna kuma kira ga masu wannan rubutu su ji tsoron Allah su daina. Muna fata Allah ya kubutar da Sheikh Ahmad Suleiman da wadanda suke tare da shi, Amin.
Mahmud Isa Yola
National Publicity Secretary, Jibwis Social Media Nigeria.

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan