WA YA SAN GOBE BANDA ALLAH BY SHEIKH ALIYU SA'ID GAMAWA
WA YA SAN GOBE.???
Nasihar wanna Rana ta Jumma'ah
Allah cikin hikimar sa ya boye mana sanin gaibi, da damar sanin mi zai faru gobe,
hakanan ba wata rai da ta san ranar ajalin sa ko garin ajalin sa.
Kuma mu tuna fa cewa: Samu da rashi, wato yalwa da rashi ko juyawar yau da gobe duk naga Allah shi kadai ubanginjin talikai.
Mu 'yan adam buri garemu da yawan tanadi, ga kwadayi da son mu samu mu tara, gamu da
sha'awa a ciki da wajen zukatan mu, da sauran
bukatun dan adam a rayuwa.
Hakika rashin sanin abinda zai faru gobe rahama ne ga dan adam kuma darassi ne garemu cewa muyi taka tsan-tsan da wannan rayuwa, mu yiwa kan mu tanadin
alheri duniya da lahira.
Ya kai dan uwa na, kada ka wulakata wani baka
san gobe mi zai zama ba. Kada ka tozarta addini don baka san kana wani aiki mutuwa zata riske ka ba. Kada kaci haramun don baka san miye abincin ka na karshe ba. Kowa ya nisanci alfasha da miyagun aiyuka don bawanda yasa aikin sa na
karahe.
Muyi don Allah mu bari don Allah cikin dukkan
aiyuka da huldodin mu na rayuwa. Mu bi hanyar Allah da ta Manzon Allah ﺹ insha Allahu ba zamu tabe ba.
Ina rokon Allah ya kara mana ilimi mai amfani, ya datsr damu natsuwa da karuwar imani, amin

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan