BAN KWANA DA SHEKARAR 1440HJR KO KETARE GADA ZUWA WATA GADA: BY Sheikh Abubakar BN Mustafa
KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: ๐29/ZUL-HIJJAH/1440HJRY ๐30/AUGUST/2019MLDY ๐MAI GABATARWA๐๐ผ Abubakar BN Mustafa Biu ๐ถTOPIC๐๐ผ (BANKWANA DA SHEKARATA 1440-HJR) ko (KETARE GADA ZUWA WATA GADA) ➖NA KASASHI GIDA 6⃣ 1⃣➖MUQADDIMA‼ Yaku bayin ALLAH! yanzu haka kafarmu daya tana kan tsohuwar gada yayinda dayar kafar kuma take kan sabuwar gada don komawa gaba daya zuwa kanta, kenan kafarmu daya na bankwana da shekara mai shudewa na 1440-hjry yayinda dayar kafar take fuskantar sabuwar shekara ta 1441-hjry, muna bankwana da cikakken shekaranda mukayi ajiyarda ALLAH yaso, taskokin wasunmu acikeda alhairi, na wasu cikeda sharri, na wasun kuma a garwaye, kuma ga sabuwar shekara, 2⃣➖WANNAN JUMA'AR‼ Wannan itace juma'ar karshe ta shekarar 1440 kuma me yiwuwa itace yinin karshen shekaran, tunda yau 29/12/1440, Yaushe muka shigo shekararnan kuma gashi har takare⁉ ๐กALLAH SW yace <<ALLAH yana jujjuya dare da rana, lalle acikin hak...