Dr. Zakir Naik Acikin Kariyar Allah. By ustaz Abubakar Umar Rigasa.
Dr. Zakir Naik acikin kariyar Allah
Dr. Zakir Naik mashahorin Malamin Addinin Musulunci ne, dan asalin kasar India, ya shiga harkar da'awa da muhawara da ma'abota Addinai kamar Nasara, Yahudu, Hindu, Sikh dama Mulhidai wadanda aka fi sani da (Atheist) a wannan zamani, bayan kammala karatunsa na likitanci a kasar ta India, ya kuma tasirantu ne da marigayi Sheikh Ahmad Deedat wanda shine ya bude kofar muhawara da Nasara a wannan karni 20 zuwa 21.
Ya samu nasarori masu yawan gaske kuma dubun-dubatar mutane ne suka shiga Addinin Musulunci ta sababinsa, bayan al'amarinsa ya daukaka ya bude cibiyar bita da nazarin Addinin Islama a kasar ta India (Islamic Research Foundation ie IRF), daga bisani ya bude tashar PeaceTV a shekarar 2012 wacce itace mafi girman tashar Addinin Musulunci da ake kallo a satellite a yankin Turai da Asia dama Africa ana kiyasta masu kallonta da million 200 ko sama da haka.
Zakir Naik ya fara fuskantar kalubale daga cikin gida India yayinda yan siyasa suka fara wasa da tunanin yan kasa akansa domin samun kaiwa ga gacci ta hanyar yi masa yarfe da kage, sun zargeshi da tsattsauran ra'ayin Addinin Islama abinda suke kira (Islamic extremists ko Islamic terrorists), daga bisani suka yi yunkurin kama shi.
Dr. Naik yayi gudun Hijira zuwa kasar Saudi acikin kafalar sarkin Salman bin AbdulAziz, sai dai bai jima ba ya bar kasar saboda a Saudia ba zai samu nishadin da'awar tasa ba kasancewar ba komai ne yake faduwa a kasar ba musanman saboda sauye-sauye siyasa da yarima me jiran gado (MBS) ya kawo kasar.
A yanzu haka Dr. Zakir Naik yana kasar Malaysia kuma ya samu jinsiyar kasar, wanda hakan yake nuna ya zama cikakken Dan kasar Malaysia a hukumance, sai dai kuma acikin wannan watan Dr. Zakir Naik yayi Lecture a kasar ta Malaysia akan abinde yake faruwa a yankin Kashmir na zaluncin India karkashin shugaban kasar dan jam'iyyar BJP masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addinin Musulunci, wanda daga bisani aka samu wasu daga cikin ministocin kasar Malaysia suka nemi ya janye wasu Maganganu da yayi da suka fassara da tsattsauran ra'ayi.
Abin takaici shine sai ga Alarabiya jaridar Saudia tana bayyana Zakir Naik a matsayin dan Ta'adda me tsattsauran ra'ayin Addinin Islama.
Lallai idan al'ummar Musulmai suka yadda suka halasta jinin wannan bawan Allah daya sadaukar da rayuwarsa saboda Addinin Allah ya samu gata to lallai sunyi babban kuskuren da zasu jima suna ganin kaskaci a duniya.
Abubakar Umar..✍️

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan