Tsakanin Malaman Musulunci Da Masana Ilimin Kimiyya Da Fasaha: by Ustadz Abdulrahaman Muh'd Sani
TSAKANIN MALAMAN MUSLUNCI DA MASANA ILIMIN KIMIYYA DA FASAHA _______________________________ _______________________________ Da yawa daga cikin wandanda suka fitinu da Turawan Yamma suke kokarin koyi da su a ko wane hali suna yawan nanata cewa addinin musulunci ko malaman muslunci suna adawa da ilimukan kimiyya da fasaha da masana wadannan ilimuka, a kokarinsu na kamanta yadda Turawan suka kasance a zamaninkan da suke kiransu da "Middle Ages" na adawa da duk wani abu da ya shafi ilimin kimiyya da fasaha da kuma yadda muslumai suka kasance ada dama yanzu. Su kan kafa hujja da yadda Malaman addinin musulunci suke daukar wasu daga cikin masana ilimin kimiyya da fasaha a tarihin musuluci wanda wannan karyace zunzurutu, manufar ita ce samawa batansu muhalli da hujja ta hanyar kiristantar da Musulunci da nuna cewa yadda Turawa basu iya samun cigaba ba sai da suka yiwa kiristanci tawaye da bore sannan suka kai inda muke gani a yau, hakanan suma muslmai sai sun yiwa addininsu taw...