Tsakanin Malaman Musulunci Da Masana Ilimin Kimiyya Da Fasaha: by Ustadz Abdulrahaman Muh'd Sani
TSAKANIN MALAMAN MUSLUNCI DA MASANA ILIMIN KIMIYYA DA FASAHA
_______________________________
_______________________________
Da yawa daga cikin wandanda suka fitinu da Turawan Yamma suke kokarin koyi da su a ko wane hali suna yawan nanata cewa addinin musulunci ko malaman muslunci suna adawa da ilimukan kimiyya da fasaha da masana wadannan ilimuka, a kokarinsu na kamanta yadda Turawan suka kasance a zamaninkan da suke kiransu da "Middle Ages" na adawa da duk wani abu da ya shafi ilimin kimiyya da fasaha da kuma yadda muslumai suka kasance ada dama yanzu. Su kan kafa hujja da yadda Malaman addinin musulunci suke daukar wasu daga cikin masana ilimin kimiyya da fasaha a tarihin musuluci wanda wannan karyace zunzurutu, manufar ita ce samawa batansu muhalli da hujja ta hanyar kiristantar da Musulunci da nuna cewa yadda Turawa basu iya samun cigaba ba sai da suka yiwa kiristanci tawaye da bore sannan suka kai inda muke gani a yau, hakanan suma muslmai sai sun yiwa addininsu tawayene zasu iya samun daukaka.
Matsayar Malaman addini dangane da wasu masana harkar kimiyya da fasaha kamar irin Su Ibnu Sina, Al'Faraby ,Ibnu Rushd, Abubakar Arrazy da makamantansu bata da alaka da irin gudunmawar da suka bayar a bangarensu, balma duk wanda yake bibiyar tarihin Malaman zai ga cewa suma suna da ido a wadannan ilimummuka wanda wannan sananne ga duk wani mai karatu da bincike, Sai dai matsayar tasu tana da alakane da wasu aikidu da ra'yoyi da wasu daga cikin wadannan masanan suka runguma wanda suka ci karo da Muslunci wannan shine ainihin dalilin da yasa malaman suka dauki matsaya mai tsaurari.
Wadancan masana Falsafar da kimiyya suna ganin cewa Allah bai halicci Duniya kai tsaye ba, suna ganin cewa Allah bai san abu filla-filla ba sai dai a dunkule ( ma'ana tauye ilimin Allah) ,suna ganin cewa babu bambanci tsakanin Annabi da philosopher kuma annabta kowama in ya dage zai iya samunta domin ba wata abace da Allah yake kebatanta wasu zababbin bayansa da ita ba, suna karyata hakikanin samuwar Wuta da Aljanna da makamanta irin wadannan ra'ayoyika na bata.
Abin mamaki shine kokarin tsuke wannan matsaya ta malamai da suka dauka akan wadannan akan iya Ibnu Taimiyya, kasancewar wannan malamin yana fuskantar adawa da tsana da daukarsa cewa shine shugaban masu tsattsauran ra'ayi, a gefe guda kuma kaga masu wannan kumfar bakin suna yabo da kokarin likewa da Abu Hamidul Ghazali kasancewar yana dangatuwa ga akidar asha'ira ya kuma taba sufanci, sun jahilci cewa shima irin matsayarsa kenan na kafurta irin wadancan masanan masu dauke da wadannan ra'ayoyuka na bata da kafurci,harma littafi yayi kacokam akan hakan wanda hakan ta sa Ibnu Rushd ya caccake shi caccaka mai tsanani shima anasa ganin ya tsaurara ya zafafa da yawa!
Lallai tabbas wadancan masana sunyi fice a bangarorin su sun kawo cigaba sosai a rayuwar dan adam bama ta iya musulmi ba kawai, ya ishemu mu san cewa su kansu Turawan yamman sun dade suna rikarsu a matsayin makoma a harakar kimiyya da fasaha da likitanci wanda akan rubuce-rubucensu ne suka iya gina cigaban da muke gani a yau.
Ko shakka babu ba don yadda dabi'ar addinin msulunci take ba na daukar ilimi da muhimmanci da karfafa gwiwar ma'abotansa da zaburar da su da su bazama don nemansa ba, da wadannan masana basu samu damar karantar wadannan ilimuka ballema su yi zarra a ciki har su amfanar, da makomarsu bata da bambanci da ta Spinoza ko Bruno ko Galileo ko Copernicus ko dai makamantasu wanda bata wuce kisa ta hanyar konawa da wuta da azabtarwa da dauri da tsinuwa da tsinewa rubuce-rubucensu ba. Watakila in dama ta samu muyi wani rubutu daban akan kwatanta halin musulmai da kuma Turawan yamma a da.
Kuma wani abun mamakin kuma shine yadda America ta kashe scientists kimanin 3000 a Iraq da yadda Isra'ila take bi tana yiwa scientists din musulmai dauki dai-daya irin su Dr Samira Musa, Dr.Yahya Almashd da Dr. Muhammad Azawawi da sauransu da yawa duk wannan batasu suke ba, wannan duk ba kokarin jahiltar da al'umma suke ba.
Iya abinda ya gabata sun isa su nunawa mai hankali yasan cewa manufar bata wuce komai ba face rusa shi kansa addinin da kirkirar wani sabo ta yadda zai dace da yadda makaya suke so.

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan