Tsokaci Game Da Chrismas: By Ustaz Abdurrahaman Muh'd Sani
TSOKACI GAME DA CHRISTMAS
___________________
___________________
Bikin Christmas shine shine biki ko idi na biyu bayan bikin Easter [1] a addinin Kiristanci, suna yinsane domin Murnar haihuwar Annabi Isa as.
Duka kungiyoyin kiristoci sun amshi wannan bikin suna kuma yinsa, sai dai akwai sabani tsakaninsu akan yaushene, a wurin masu bin Gregorian Calendar[2] 25 ga watan December, a wurin mabiya Julian Calendar [3] kuma 7 ga watan January.
Wannan bikin ba'a farashi ba sai a shekara ta 325 C.E aka kirkireshi aka misanyashi da bikin maguzancin da Rumawa suke a daidai wannan ranar, hakan ta farune a wannan shahararren taronan da ake kira da firts council of Nicaea, wanda a wannan taron ne suka aka tabbatar da Allantakar Annabi Isa As, duk da cewa mafi yawan malamansu na lokacin sun ki yarda da hakan Amma kasancewar wannan shine ra'ayin sarkin Rumawa na lokacin wato Emperor Constantine The Great aka zartar da hakan.
Kamar al'adar ko wane kagaggen abu haka aka shiga yiwa wannan bikin kare-kare kamar tsohon da mai jajayen kaya da yake yawo yana bawa yara kyautuka wanda ake kira da Santa Claus wand asalinsa wani pastor ne da akayi a baya, da kuma bishiyar biki wato Christmas Tree wanda ta samu asaline daga bukukuwan fir'aunonin Masar da al'umomin Yankin Gabas ta tsakiya na da da kuma maguzawan Germany wanda da suka tashi shiga kiristancine suka shigo da ita, hakanan raba kyauta kuma ya samo asaline daga wani bikin maguzanci na godiya da Rumawa suke yiwa wani abin bautarsu da suke kira da Saturlinia
Malaman Muslunci na mazhabobi guda 4 sun tafi akan haramcin aiwatar da wannan biki ko taya kiristoci murnar wannan biki kasancewar kamar kara taimakonsune da goyamusu baya akan kafiricinsu da batansu wannan maganar tanan a littafan malamai a rubuce a haka kuma akayi ta tafiya babu wanda ya tafi akan sabanin haka.
A wannan zamanin kasancewar Muslmai suna fama da rauni da kuma karfin tasiri da ruwada da wayewar Turawan Yamma aka samu wasu suna kokarin hallata taya kiristoci muranar wannan rana harma da taimakonsu duk da sunan zamantar da Addini da wayewa da kuma zamana lafiya da lumana.
Lallai duk wanda ya kalli shi kansa Tarihin wannan biki da ma sauran bukukuwan addini nasu zai ga cewa a addinin kiristancin ma bashi da asali ya kuma samo asaline daga maguzanci , kuma zai ga cew su kansu sun gagara kiyaye addininsu ina kuma ballantana su kiyaye wanda suke jinginawa wannan addinin shiyasama suka tayi sabani
Hukunce-hukuncen Musulunci bana misaye bane bane don haka baya hallata taya kirisita murnar haihuwar wanda yake gani dan Allah ne ko da shi ya taya Musulmai muranar nasu Idin, domin kasancewar bamaguje ya girmama masallaci ba shi zai sa ka girmama Gunki ba, kasancewar An hallatawa muslmi ya auri bakitabiya ba shi zai sa a aurawa bakitabe Muslma ba.
Kuma Lallai mu san cewa kyautawawa da zaman lafiya baya nufin mu saki addinin mu mu narke mu zama wasu abinda in kyautawawa ake nema da kuma zaman lafiya to abi tsarin da Muslunci ya kawo ba tsarin wasu daban ba.
=================
[1] bikine da kiristoci suke yi na tashin Annabi da komawa sama bayan bayan gicciyasa da binnesa da kwana 3
[2] Gregorian Caledar itace wacce Kiristocin Yamma su Catholic da Protestants suke
[3] Julian Calendar itace wacce kiristocin Gabas suke bi kamar su Orthodox tana bayan Gregorian Calendar da kwana 13.

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan