Posts

Showing posts from December, 2019

Tsokaci Game Da Chrismas: By Ustaz Abdurrahaman Muh'd Sani

Image
TSOKACI GAME DA CHRISTMAS ___________________ ___________________ Bikin Christmas shine shine biki ko idi na biyu bayan bikin Easter [1] a addinin Kiristanci, suna yinsane domin Murnar haihuwar Annabi Isa as. Duka kungiyoyin kiristoci sun amshi wannan bikin suna kuma yinsa, sai dai akwai sabani tsakaninsu akan yaushene, a wurin masu bin Gregorian Calendar[2] 25 ga watan December, a wurin mabiya Julian Calendar [3] kuma 7 ga watan January. Wannan bikin ba'a farashi ba sai a shekara ta 325 C.E aka kirkireshi aka misanyashi da bikin maguzancin da Rumawa suke a daidai wannan ranar, hakan ta farune a wannan shahararren taronan da ake kira da firts council of Nicaea, wanda a wannan taron ne suka aka tabbatar da Allantakar Annabi Isa As, duk da cewa mafi yawan malamansu na lokacin sun ki yarda da hakan Amma kasancewar wannan shine ra'ayin sarkin Rumawa na lokacin wato Emperor Constantine The Great aka zartar da hakan. Kamar al'adar ko wane kagaggen abu haka aka shiga y...

CIKIN KOMI AKWAI ALA'MA DA YAKE GWADA SAMUWAN ALLAH: BY USTAZ AHMAD MUHAMMAD MAKAMA

Image
Cikin komi akwai ala'ma da yake gwada samuwan Allah da cancantar sa shi kaɗai a matsayin Abun bauta. Duk wata al'umma da take rayuwa a doron duniya za ka sa mu a cikin su akwai wanda dogon mutum ne, wani gajere wani me ƙiba wani siriri. Akwai hikima cikakke cikin yadda Allah ya tsara halittan mu, da duk Allah yayi mu gajeru to da an samu naƙasu a rayuwa don dole a samu ayyukan da dole sai dogaye ne za su iya, haka da duk anyi mu dogaye shima da na sa matsalan, haka yake tsakanin siraran mutane da ma su ƙiba, da ƙarfafa da masu rauni ko wanne yana bukatan ɗan uwan sa don wanzuwan rayuwa a tsakanin su. Ta Ha 20:50 قَالَ رَبُّنَا ٱلَّذِىٓ أَعْطَىٰ كُلَّ شَىْءٍ خَلْقَهُۥ ثُمَّ هَدَىٰ He said, "Our Lord is He who gave each thing its form and then guided [it]." Ba wata hankali da za ta yarda ta amince cewa wannan rarrabuwan halittan ya faru ne haka kawai ba wanda ya tsara. Haka yake wajen rarrabuwan sana'a da fannoni na ilimi da mulki, ko za a kashe wani ba...