Minister Dr.Isa Ali Ibrahim Pantami Ya bawa shuwagabannin Hukumuminnsa 6: By legit Hausa

Minista Dr Isa Pantami ya ba shugabannin Hukumominsa 6 aikin da za su yi masa nan take

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto jiya, 1 ga Watan Satumba, 2019, Isa Pantami ya bayyana wannan ne a Hedikwatarsa a birnin tarayya Abuja inda yi kira ga CEO da Darektocin su tashi tsaye.

Dama can Ministan ya bayyana cewa za a sanyawa kowace ma’aikata aikin da ake so ta yi zuwa wani lokaci, inda za a rika bibiyan kokarin da kowane shugaba ya ke yi domin sauke nauyin da ke kansa.

1. Kamfanin Galaxy Backbone

Daga cikin aikin da aka ba wannan kamfani shi ne su gyara karfin layinsu da sauran ayyukan da su ke yi wa jama’a.

2. Hukumar NCC

Ma’aikatar sadarwa ta ba NCC lokaci ta kawo karshen matsalar rashin yi wa layukan waya cikakken rajista wanda hakan zai inganta matsalar rashin tsaro. An kuma nemi NCC ta duba yadda ake zaftarewa jama’a kundin hawa yanar gizo tare da rage farashin na data da kuma waya.

3. Hukumar NIGCOMSAT

Hukumar NIGCOMSAT mai kula da faifen satalait na Najeriya na da aikin gyara karfin na’urarta domin hasko fadin kasar da kyau kamar yadda sabon Ministan kasar ya gindaya mata a jiya.

Isa Pantami ya nemi magajinsa a NITDA ya dage wajen ganin an samu karuwar masu amfani da na’urorin gafaka da manhajojin gida a ma’aikatu. Ana kuma so ma’aikatu su rika amfani da na’urorin zamani wajen aikinsu.

5. Hukumar NIPOST

Sabon Ministan sadarwa ya nemi NIPOST ta kara kokari wajen aika sakonni da wasiku a fadin kasar. Isa Ali Pantami ya kuma bada umarni ga hukumar ta kara yawon wuraren da ta ke shiga.

6. Hukumar USPF

A karshe mai girma Ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami bai bar ma’aikatar USPF da ke karkashinsa a baya ba, inda ya nemi ta rage tazarar da ake samu wajen aiki tsakanin Birane da karkara.

Jaridar legit Hausa ce ta ruwaito haka daga Jaridar Daily Nigeria .

Muhammad Ismail Ali.

Comments

Popular posts from this blog

MEKE FARUWA A KANO: By Dr. BELLO GALADANCHI KANO

Shin Ya dace Bulama Bukarti Ya kira abinda Bauchi state Governor ya fada da wawanci? By: Muhammad Shu'aibu Gunda

WAIWAYE ADON TAFIYA (4) by USTAZ ABDURRAHAMAN MUH'D SANI RIJIYAR LEMO