Khudabar Masjidis Salafiyya: by Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu
KHUDUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐13/MUHARRAM/1441-HJRY
🌐13/SEPTEMBER/2019-MLDY
🎙MAI GABATARWA👉🏼 Abubakar BN Mustafa Biu
🔶TOPIC👉🏼 [[MASU BOYEWA]]
➖MUN KASASHI GIDA (12) 👉🏼
1⃣➖MUQADDIMA:
Yaku bayin ALLAH! muni tsoron murika nazarin Hadisinnan da ANNABI SAW kecewa <<ALLAH yanason bawa mai taqawa da wadatar zuci da boyewa (yin ibada aboye)> {MSLM}
2⃣➖WANENE MAI BOYEWANDA ALLAH KE SON NASAN⁉
Sune masu aiwatarda wasu ibada amatsayin sirri tsakaninsu da ALLAH, Masu sallolin nafilfili aboye, Masu sadakawa Fakirai da miskinai da marasa galihu da marayu da gajiyayyu a boye, ba abinda yasa suke boyewa face don kada riya tabata musu ladan aikin,
3⃣➖DONME ZAMUYI MAGANA AKAN MASU BOYEWA⁉
Dalili kuwa shine💡ANNABI SAW yace <mutum 3 dasu za'a fara hura wutar Jahannama don sunyi riya= ¹ Makarancin Qur'ani ² Mai jihadi ³ Mai sadaka,
Da MU'AWIYYA R/A yaji Hadisinnan sai yafashe da kuka kuma yace= HMMMMM! idan haka za'ayi da wadannan ukun- to yaya za'ayi da sauran mutanen⁉ yacigaba da kuka har aka zaci zai mutune‼
4⃣➖BOYEWA A QUR'ANI:
💡ALLAH SW yace <<Ku kira UBANGIJINKU da kaskantarda kai d BOYEWA>>
💡ALLAH SW yace <<in kun BOYE sadaka kuka bawa Fakirai to yafi alhairi agareku>> IBN HAJAR yace= wannan ayar yanuna afili fifikon sadakar BOYE,
5⃣➖BOYEWA A HADISI:
💡ANNABI SAW cikin mutum 7 daza'a inuwantar dasu a inuwar al'arshi yace➖da <Wanda yatunada ALLAH a BOYE sai idanunsa suka zubda kwalla>➖kuma yace <da wanda yayi sadaka aboye har damansa baisan meye hagunsa yabayarba> {BHR & MSLM} IBN HAJAR yace= wannan shine mafi karfin dalilan dake nuna fifikon sadakar BOYE!
6⃣➖MASU BOYEWA A SADAKA:
◼UMAR IBN KHATDAB R/A yashiga wani gida aboye cikin dare, sai TDALHA R/A yaganshi sai yazo gidan da safe sai yatararda tsohuwace agidan kullum sai UMAR yazo ya tsabtaceta da kuma daukan nauyinta,
◼Hakama ZAINUL ABIDEEN- ALIY IBN HUSAIN R/A yakan dauki buhunan abinci agadon bayansa aboye cikin dare yarika rabawa Fakirai, da akazo masa wankar gawa sai akaga kantar dako abayansa sai aka gane shine, BABAN IBN ABI AISHA yace= 'yan Madina sukace= bamu rasa sadakar sirriba saida ALIY IBN HUSAIN yarasu,
(سير أعلام النبلاء/صفوة الصفوة)
7⃣➖MASU BOYEWA DA SALLA:
◼BAKAR IBN MA'IZ yace= Ba'a taba ganin RABEE'U yana nafila a masallaciba sai sau daya rak,
◼HASAN IBN SINAN yakan shiga mayafin matarsa yalallabeta tayi barci saiya sulale yadda uwa kewa jariri- sai yaje yafara kiyamullaili, rannan tace dashi= Katausayawa kanka! donme kake azabta kanka? Sai yace= Kaitonki! saura kiris inyi kwanciyarda zanyi tsawon lokaci ban tashiba!
8⃣➖MASU BOYEWA DA AZUMI:
◼DAWUD IBN ABI HIND tsawon shekaru 40 yana azumin nafila matarsa bata saniba, zai fita da abincinsa zuwa wurin sana'arsa sai yasadakar a hanya, ➖kuma wasu na shafa mai a lebbansu don kada agane suna azumi (سير أعلام النبلاء)
9⃣➖MASU BOYEWA DA KARATUN QUR'ANI:
◼RABEE'U in yabude QUR'ANI yana karantawa sai wani yashigo sai yalullube Qur'anin da tufarsa yaboye (صفوة الصفوة)
🔟➖MASU BOYEWA DA KUKA:
◼MUHD IBN WASI'U yake cewa= na riski wasu mutane- dayansu zaiyi shekara 20 kullum sai yayi kukan tsoron ALLAH yajika filo shakaf amma matarsa bata saniba alhali kansu su biyu yana kan filon, Kuma na riski wasu mutane dayansu zaiyi kuka a salla alhali wanda suka hada sahu tare bai saniba,
◼ABU AYYUBAS SAKHTIYANY yana Majalisi sai hawayen tsoron ALLAH yazubo masa, sai yawayence yayi kaki yace= Kai! akwai mura! (سير أعلام النبلاء)
11➖MASU BOYEWA DA WALLAFA ILIMI:
◼IBN KHALKAN yace= IMAM MAWURDY- Litattafanda yawallafa babu guda daya da yabayyana sai bayan mutuwarsa, kafin yamutu yakira wani amintaccen mutum yace dashi= inada litattafanda na wallafasu awuri kaza, kazauna awurina idan magagin mutuwa yazo mini to kasa hannunka acikin tafin hannuna idan kaji inata matsa hannunka to ALLAH bai karbi aikin rubuta litattafanba- don haka sai katattarosu aboye cikin dare kaje kawatsar dasu akogi, amma in ban matsa hannunba har namutu to kasan nayi nasarar niyyata ALLAH yakarba- sai abuga litattafan agabatarwa duniya,
Da magagin mutuwar yazo sai bai matse hannunba sai mutumin yagana cewa ALLAH yakarba,
◼IMAM SHAFI'IY yace= Naso ace masu karanta ilmukana sukarantar batareda jinginashi gareniba don samun ladana cikakke batareda nakasu don yabo ba!
12➖RUFEWA- HALINMU A YAU‼
Abin takaici al'ummar musulmai ayau mun wayi gari mun sabawa Magabatanmu, mun zanto MASU BOYE SHARRI, Muna tsafi, zina, luwadi da madigo aboye, SUBHANALLAH‼babban abin haushin ma- sace sacen mutane da kashe kashe ajihohin ZAMFARA, KATSINA, SOKOTO, KANO, BORNO, YOBE da sauran jihohin Musulmai- zama tarar mai wannan aika aika- da Wanda yasa ayi- da wanda yataimaka ayi- da wanda akayi akansa- duk Musulmaine masu magana da yare daya😭 INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UUUN😭‼
👏🏼YA ALLAH! KASAMU CIKIN MASU AIKATA DUMBIN ALHAIRAI ABOYE DA IKHLASI👏🏼
Amiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiin👏🏼👏🏼👏🏼
via👉🏼 Sheikh
Abubakar BN Mustafa Biu✍🏽

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan