SALLAR IDI DA WASU HUKUNCE-HUKUNCEN SA BY SHEIKH ALIYU SA'ID GAMAWA
*SALLAR IDI DA WASU HUKUNCE-HUKUNCENSA !!!*
.
*SALLAR IDI:* Sunnah ce mai qarfi akan wanda sallar jumma'a ke wajaba akansa wato mace ko namiji baligi, mai hankali, lafiyayye daga dukkanin cututtuka ko uzurori masu hana shi halartar sallar idi.
.
*LOKACIN SALLAR IDI:*
.
Lokacin sallar idi yana farawa ne a lokacin da rana ta 6ullo tayi sama, gorgodon tsawon mashi d'aya ko biyu, kuma yana qarewa kafin rana ta karkata daga tsakiyar sama wato kafin lokacin sallar azahar.
.
*WAJEN DA YAKAMATA AYI SALLAR IDI:*
.
Yana daga Sunnah musulmai suyi sallar idi awajen gari (wato bayan gari) idan har hakan zai yuwu ba tare da wata Matsala ba.
.
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya kasance yana barin masallacinsa ya fita zuwa daji tare da mutane yayi sallar idi tare dasu. Duk da kasancewar masallacinsa yafi ko ina falala a garin madina.
.
Abu-sa'id Alkhudri yace: "Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya kasance yana fita bakin daji a sahara ranar Idul Fidr da Idul Adhaa zuwa masallaci, sallah ita ce farkon abunda yake fara yi" [Bukhari da Muslim @kitabus siyaam]
.
*ABUBUWAN DA SUKA KE'BANTU GA SALLAR IDI:*
.
1• *ADADIN RAKA'O'IN SALLAR IDI DA KABBARORINTA:* Sallar idi raka'ah biyu ce , za'ayi kabbara bakwai kafin fara karatun liman a raka'ah ta farko, a raka'ah ta biyu kuma za'ayi kabbarori biyar bayan kabbarar tsayuwa.
.
Saboda abunda yazo daga Dan Umar (RA) yace: " Na halarci sallar idul fidr da idul Adha tare da Abu-hurayrah (RA) sai yayi kabbarori bakwai a raka'a ta farko kafin ya fara karatu, a raka'a ta biyu kuma sai yayi kabbarori biyar kafin ya fara karatu"
.
2• *QIRAN SALLAH KO TADA IQAMAH A SALLAR IDI:* sallar idi bata da qiran sallah ko iqamah, Ijma'in malamai ya tabbatar da wannan. Saboda fadar Abdullahi Dan Abbas da Jabir Dan Abdullahi (RA) sunce: Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) bai ta6a yin qiran sallah ko iqamah ba a sallolin idi" [Bukhari da Muslim daga Hadithin Dan Abbas]
.
3• *KARATUN SALLAR IDI*: Bayan karatun Fatiha liman yana da damar ya karanta abinda yake so na Alqur'ani a sallar idi bisa ijma'in malamai.
.
Saboda ALLAH (SWT) Yace: "ku karanta abunda ya sauqaqa agare ku daga cikin alqur'ani".[Surah 73:20]
.
Hadith yazo daga Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya kasance yana karanta suratul A'ala a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma suratul Ghashiyah" kuma ya inganta cewa wani lokaci yana karanta suratul Qaaf a raka'a ta farko, a raka'a ta biyu kuma suratul qamar [Ahmad, Dabarani da Muslim sun ruwaito shi daga Hamza Dan jundubi]
.
4• *HUDUBAR SALLAR IDI:* Yin hud'uba a sallar idi Sunnah ce haka sauraron hud'ubar ma Sunnah ce, ana yinta ne bayan an idar da sallar. Kamar yadda hadisin Abu sa'id Alkhdri ya tabbatar cewa:..... "_sannan bayan sallah mutane na Zaune a sahu sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya juyo ya fuskance su yayi musu wa'azi da wasiyya sannan yayi musu umurni da alkhayri da hani ga miyagun ayyuka"
.
Hakanan ba a qayyade hud'ubar sallar idi ba liman yana da damar yayi hud'uba yadda ta sauwaqa.
.
5• *KABBARORI A RANAR SALLAR IDI:* kabbaori a ranar sallar ana fara sune daga bayan sallar asubah ta ranar farko ga watan Shawwal har zuwa lokacin sallar idi.
.
→Lafazin kabbarorin shine: *"ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, LA'ILAHA ILLALLAHU, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, WALILLAHIL HAMDU"*
.
Ya tabbata sahabbai suna yi a ranar d'aya ga watan Shawwal da kwanaki uku bayan sallah.
.
*6• ZUWA SALLAR IDI DA DAWOWA DAGA IDI*: shine mai zuwa sallar idi ya dawo daga idi bata hanyar da yabi yaje ba, hadith ya tabbata daga Jabir Dan Abdullah (R.A)
.
*ABUBUWAN DA AKE BUQATA KAFIN ZUWA SALLAR IDI:*
.
★ Ana son ayi wanka a Sanya turare kuma ayi ado da sabbin tufafi ko kuma tufafi mai kyau koda ba sabo bane, kafin zuwa sallar idi.
.
★ Ana so aci abinci asha abunsha kafin a fita zuwa sallar idi.
.
★ Ana son ayi gaggawa wajen fitar da zakkar fidda kai kafin ayi sallar idi.
.
★ Ana so a tafi zuwa idi da qafa bada abun hawa ba sai dai idan da wani uzuri, kuma ana son a tafi zuwa idi cikin nutsuwa.
.
*ALHAMDULILLAH ALLAH YA AMSA MANA IBADUNMU YA NUNA MANA LOKACIN IDI LAFIYA (Ameen)*

Comments
Post a Comment
Rubuta "comment" Anan