Posts

Showing posts from June, 2019

SALLAR IDI DA WASU HUKUNCE-HUKUNCEN SA BY SHEIKH ALIYU SA'ID GAMAWA

Image
*SALLAR IDI DA WASU HUKUNCE-HUKUNCENSA !!!* . *SALLAR IDI:* Sunnah ce mai qarfi akan wanda sallar jumma'a ke wajaba akansa wato mace ko namiji baligi, mai hankali, lafiyayye daga dukkanin cututtuka ko uzurori masu hana shi halartar sallar idi. . *LOKACIN SALLAR IDI:* . Lokacin sallar idi yana farawa ne a lokacin da rana ta 6ullo tayi sama, gorgodon tsawon mashi d'aya ko biyu, kuma yana qarewa kafin rana ta karkata daga tsakiyar sama wato kafin lokacin sallar azahar. . *WAJEN DA YAKAMATA AYI SALLAR IDI:* . Yana daga Sunnah musulmai suyi sallar idi awajen gari (wato bayan gari) idan har hakan zai yuwu ba tare da wata Matsala ba. . Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya kasance yana barin masallacinsa ya fita zuwa daji tare da mutane yayi sallar idi tare dasu. Duk da kasancewar masallacinsa yafi ko ina falala a garin madina. . Abu-sa'id Alkhudri yace: "Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya kasance yana fita bakin daji a sahara ranar Idul Fidr da...