Hanya ɗaya tilo ta kawo karshen almajirinci a Arewacin Najeriya: by Ado Abdullahi
Hanya ɗaya tilo ta kawo ƙarshen almajiranci a Arewacin Nijeriya Daga Ado Abdullahi Idan ban manta shekarar ba, ina tsammanin a wajejen 2005-2006 ne. Wani abokina ya gayyace ni zuwa taron wata ƙungiyarsu da suka kafa domin taimakawa al’majirai ta hanyar ɗinka musu sutura da raba musu sabulan wanka. Duk da bayar da wannan gudunmawa, ƙungiyar tana nuna rashin jin daɗinta da rashin dacewar yadda iyayen yara musamman daga ƙauyuka suke tuttuɗo ƙananan yara inda wasun su ba su wuce shekaru uku da haihuwa ba, zuwa birane da sunan zuwa karatun allo. Wanda a ƙarshe suke ɓugewa da barace-barace da gararamba a tituna cikin ƙazanta, yunwa ga kuma uwa-uba rashin tarbiyya. Wani lokaci su ake amfani da su wajen tayar -da -zaune -tsaye domin biyan muradun ƴan siyasa. Lallai a lokacin na yaba da yadda suka tashi tuƙuru wajen bayar da tasu gudunmawar wajen taimakon makarantun allon. Duk da dai daga baya na nuna musu kuskuren yin haka. Ba wai domin taimakawa masu...